Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar ta ce dakarunta da ke Baale kusa da Damboa ne suka ceto yarinyar.
Sai dai bai yi karin bayani kan hakan ba.
Tun da farko bayanai da ke fitowa daga Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke arewacin Najeriya, na cewa an samu wata yarinya daga cikin 'yan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.
Wata mai fafutuka kuma farfesa a jami'ar Maiduguri, Hauwa Biu ce ta tabbatar wa BBC wannan labari.
Farfesa Biu ta ce an gano yarinyar ne sakamakon wata arangama tsakanin 'yan kato da gora da mayakan Boko Haram a kusa da dajin Sambisa.
'Yan kato da gorar sun samu nasarar fatattakar mayakan Boko Haram din, amma sun samu wata yarinya a tare da su da goyo a bayanta.
Daya daga cikin 'yan kato da gorar ne ya gane yarinyar a matsayin daya daga cikin 'yan mata makarantar sakandaren Chibok da aka sace a shekarar 2014.
Farfesa Biu ta ce, "Sai suka kwace yarinyar daga hannun mayakan suka kai ta garin Chibok kuma iyayenta sun gane ta.''
Yanzu haka dai yarinyar tana hannun sojoji a garin Dambuwa, har sai an kammala duk wani bincike da ya kamata a yi.288